AJALI: Garin guje wa jami’an kiyaye hadura, ya kade yar shekara 2 har lahira …

HASSAN TURAKI.

Wani direban motar bas ya murƙushe wata yarinya ’yar shekara biyu a ƙoƙarin gujewa kamun jami’an hukumar kare haƙƙin jama’a na Jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a kan titin Ring Road da ke birnin Benin a ranar Laraba lokacin da jami’an hukumar suka yi artabu da wani direban motar bas a lokacin da suke ƙoƙarin kama shi.

Shaidu sun ce lamarin ya ta’azzara ne a lokacin da jami’an da ke aikin suka tunkari direban inda yake ƙoƙarin tserewa ya sauya hanyar motar, amma jami’an sun kama sitiyarin motar.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Edo, Moses Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace, jami’in tsaron da ake zargi da haddasa haɗarin tare da direban a yanzu haka suna hannun ’yan sanda domin gudanar da bincike.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *