JIGAWA: Majalisar zartarwa ta ware naira miliyan 1,000 da miliyan 800 da 82 …

SALEH UMAR ANDAZA.


Majalissar zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bada rancen kudi sama da naira miliyan dubu daya da miliyan dari takwas da tamanin da biyu ga hukumar jin daɗin alhazai ta jiha domin kammala shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jiha, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalissar da Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati.
Ya bayyana cewa majalisar ta amince da bayar da rancen kudaden ne domin bai wa hukumar damar biyan ragowar biyace biyacen maniyatan aikin hajjin bana kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa ta bukata.
Alhaji Sagir Ahmed ya ce majalisar ta amince da fitar da kudi sama da miliyan dari shida da takwas domin gina cibiyar horar da sana’o’i na fasaha a ƙaramar hukumar Garki.
Ya bayyana cewa cibiyar za ta bai wa matasa damar koyon sana’o’i da fasahohin zamani domin inganta rayuwar su.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *