HASSAN TURAKI.
Wata mata ta kashe kishiyar ta bayan sheka mata ruwan zafi da ya illata rayuwar ta.
shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar yan sandan jihar Jigawa SP Lawan Shi’isu Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutaccen sako da ya aike wa manema labarai.
Matar me suna Rukayya Adamu me shekaru ashirin da haihuwa yar asalin kauyen Buju dake karamar hukumar Dutse ta sheka ma kishiyar ta me suna Asiyah Ahmadu yar shekara talatin 30nruwan zafi sakamakon rashin fahimtar da ya faru a tsakanin su.
Hakan ya sanya Asiyah samun mummunan raunuka a jikin ta.
Yan sanda sunyi hanzarin garzaya wa da ita babban asibitin dutse domin ceto rayuwar ta inda babban likita ya tabbatar da rasuwar ta a ranar 04/03/2025 yayin da take karbar magani.
Tuni dai wacce ake zargi ta amsa laifin ta a sashin bincike dake babban ofishin yan sanda na dutse, kuma zata gurfana a gaban kuliya manta sabo domin karbar tukuicin doka.
Leave a Reply