BATURE Vs. JOBE: Ana cigaba da dambarwar siyasa a Dawakin tofa,Tofa da rimin gado …

Mukhtar Shu’aibu D/tofa.

Kakakin Gwamnan Kano Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi sukuwa da zamiya ta siyasa a kan Ɗan Majalisar Tarayya na Dawakin Tofa, Tofa da Rimingado wato Tijjani Abdulkadir Joɓe.

A cikin wani saƙo da Sunusin ya wallafa a shafin sa na Facebook ya caccaka Joɓen har ma ya daki ƙirji game da raɗe-raɗin da aka jima ana yi na cewa zai sake neman takarar Majalisar Tarayya a 2027

Daukar ɗumin wannan dambarwa ya biyo bayan bidiyon Abba Ganduje da Sunusi Bature ya yaɗa a shafin sa na Facebook tare da yabon sa, abin da ake zargin bai yiwa Joɓen daɗi ba.

Kafin zaɓen 2023 dai an ga Fastocin Sunusin na neman takarar Majalisar Tarayya sai dai a lokacin da G7 ta rushe Joɓe ya shigo Kwankwasiyya Bature ya ajiye sannan ya marawa Joɓe baya wanda yana cikin manyan ƴan siyasa da suka bada gudummawa wajen nasarar Joɓen.

Kuma tun bayan zaɓen an samu kiraye-kiraye daga al’umma mabanbanta a ƙananan hukumomin na neman Sunusin ya sake fitowa neman takarar, to amma za’a iya cewa wannan shi ne karon farko da Sunusin ya ayyana takarar ƙarara ga jama’a.

Sunusi Bature dai na cikin manya-manyan na hannun daman Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf masu ƙarfin faɗa aji cikin kunshi gwamnati.

Sunusi Abdulƙadir Joɓe, yana cikin jerin ƴan majalisar tarayya da suka ja daga da Gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a lokacin da yake kan mulki.

Joɓe yana cikin jagororin da suka kafa tsagin APC G7 wanda aka sha artabun siyasa da su.

Daga ƙarshe Joɓe ya shigo Kwankwasiyya inda ya yi takarar Majalisar tarayya sannan ya bada gudunmawa matuƙa wajen samun nasarar jam’iyyar NNPP har aka kafa Gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf.

A gefe guda dai jam’iyyar adawa ta APC har yanzu ɗan tsohon Gwamna Ganduje Engr. Abba Ganduje shi ake hasashen za ta sake bai wa tikitin takara a 2027.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *