Hassan Turaki.
Shugaban kungiyar masu bukata ta musamman na karamar Hukumar Jahun Malam Wada Jahun ne yabayyana haka a ranar Juma’a yayin da shugaban karamar Hukumar Jahun Hon. Jamilu Muhammad Danmalam yake mika tallafin kayan abinci da kudade ga mambobin kungiyar a sakatariyar mulki ta karamar Hukumar.
Mal. Wada yace yazama dole su yaba da kokari da jajircewar shugaban bisa yadda yake share musu hawayen su a duk lokacin da suka bukata.
Yayin dayake kaddamar da rabon kayan Abincin Azumi ga masu bukata ta musamman, shugaban karamar Hukumar hon. Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana masu bukata ta musamman da cewa ba Wani laifi su kayi wa Allah ya halicce su haka ba, Dan haka suma suna da hakki a gurin shugaba kamar sauran jama’a.
Hon. Danmalam yace an zabo rukunin masu bukata ta musamman har mutum dari biyu da ashirin (220). Daga mazabu goma Sha Daya (11) dake fadin karamar Hukumar domin tallafa musu da ihsanin azumi
Yayin da kowannen su ya sami tallafin taliya katon Daya, da buhun shinkafa, da tsabar kudi Naira dubu biyar (5000)
Shugaban ya bukaci da susaka karamar Hukumar Jahun da Jihar Jigawa cikin addu’o’in su musamman cikin wannan wata Mai Alfarma
A jawaban su daban-daban mataimakin shugaban karamar Hukumar Jahun Hon Rabi’u Salisu Harbo, da daraktan kudi da mulki ALH. Yakubu bala sunce sai da shugaban karamar Hukumar ya nemi shawarar su da amincewar kansiloli Kafin aiwatar da rabon tallafin.
Signed:
Ismael Salisu Bature Jahun
Mai baiwa shugaban karamar hukumar jahun shawara akan harkokin yada labarai.
08-03-25.
Leave a Reply