VILLA: Shugaban kasa ya nada Attahiru Jega …

Hassan Turaki.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba shi shawara kuma kodineta kwamitin sabon tsarin gyara fasalin kiwon dabbobi na Shugaban Kasa.

Sanarwar nadin na ɗauke da fatan shugaban ƙasa na samar da ci gaba mai ma’ana a fannin kiwo da kuma kara karfafa ayyukan ci gaban kasa.

Idan ba’a manta ba, Farfesa Jega, wanda tsohon jagora ne a jami’ar Bayero inda ya rike mukamin (Vice Chancellor), shi ne ya jagoranci kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan sake fasalin tsarin kiwon dabbobi, kwamitin da ya bayar da shawarwarin da suka kawo sabbin sauye-sauyen da ya haifar da kafa ma’aikatar Kiwon dabbobi har da samar da minista.

Naɗin nasa a matsayin mai ba Shugaba Tinubu shawara na musamman zai karfafa nasarorin da kwamitin shugaban kasa ya samu tare da tabbatar da ci gaba da sauye-sauyen da tuni aka fara aiwatarwa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *