Hassan Turaki.
Rundunar ’yan sandan Najeriya tace ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Najeriya me suna David Shikfu Parradang, a ɗakin wani otel.
A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, tace tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel saɓanin rahoton dake cewa masu garkuwa da mutane ne suka kashe shi.
Adeh tace rasuwar Mista Parradang na zuwa ne bayan yayi wata baƙuwa mace da ta kai masa ziyara ɗakin otel ɗin ya kama na kwana guda.
Leave a Reply