Daga Hassan R Jibrin.
Wasu matasa a Kasar Indiya, biyo bayan wani shagube da Babban Alkalin kasar, Mai Shariya Sury Kanta, yayi a lokacin sauraron wata shariyar karatun digiri na bogi da cewar matasa kamar kyankyasai suke.
Matashi Abhijeet Dipke, ya mayar da martani ta hanyar kafa jam’iyya mai sunan Cockroach Peoples Party.
Sabuwar jam’iyyar kawo yanzu tana neman shallake Jam’iyyar BJP mai mulkin Kasar ta Indiya, a yawan magoya baya da suka kai mutane miliyan goma.
Ana sa ran jam’iyyar ta Kyankyasun wato CPP gudanar da taron ta na farko da wakilai sama da dubu talatin da biyar










