BAUCHI: An samu siminti a jihar Bauchi …

Hassan Turaki.

Bayan gano dumbin arzikin danyen man fetur da Iskar gas, a yau jihar Bauchi ta shiga jerin jihohin dake samar da siminti.

Hakan ya biyo bayan ƙaddamar da haƙo Ma’adanan dutsen limestone a yankin Diji dake kasar Gwana a ƙaramar Hukumar Alkaleri wanda gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya jagoranta.

A na sa ran samar da ayyukan yi wa mutane sama da dubu goma sakamakon wannan aikin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *