BAUCHI: Alhaji Nuru ya shiga hanun hukuma sakamakon kashe matar sa …

Hassan Turaki.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ta Kama Wani Dan Kasuwa Bisa Zargin Kashe Matarsa Kan Rabon Kayan Bude Baki

Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta rabawa manema labarai dauke da sa hannun Kakakin Rundunar CSP Ahmed Mohammed Wakil, da karfe 11:30 na dare ne aka ja hankalin rundunar kan zargin kisan kai a unguwar Fadaman Mada.

Lamarin ya faru ne sakamakon rashin fahimta da ya shiga tsakanin magidancin mai suna Alhaji Nuru Isah, dan kimanin shekaru 50 da haihuwa da matarsa ta biyu mai suna Wasila Abdullahi ‘yar kimanin shekaru 24, kan kulawa da kayan abinci da kayan marmari da aka tsara rabawa domin buda baki, wanda hakan ya kai ga mummunar rikici.

Binciken farko ya nuna cewa, wanda ake zargin wato Alhaji Nuru Isah yayi amfani da bulala ne wajen zane matarsa, wanda hakan yasa ta fita daga hayyacinta, har aka garzaya da ita Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda likita ya tabbatar da mutuwar ta.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama Alhaji Nuru Isah, yayin da aka gano bulalar da yayi amfani da ita kuma za’a yi amfani da ita a matsayin shaida, inda gawar Wasila kuma aka ajiyeta a wajen ajiye gawarwaki domin gudanar da bincike.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *