Hassan Turaki.
Al’umar jihar Jigawa sunyi godiya da fatan alkhairi ga Hon. Abba Muhammad Mukhtar jigo a jam’iyyar APC.
Abba ya samu yabo ne da jinjina sakamakon kokarin sa na raba makudan kudade ga al’uma ba tare da nuna banbancin jam’iyya ba.
Wakilin GuaranteeNews ya gana da wadan da suka samu wannan kabakin alkhari harma wani da ya nemi a sakaye sunan sa yace “Abba ya share min hawaye, bani da abinda zan sayi geron kunu amma yanzu na samu kudin da zan sayi shinkafa”
Abba yayi kira ga al’uma da su dage da adduo’in nema wa kasa haɓakar tattalin arziki, tare da yiwa shugabanni addu’a mamakon malamai marassa daɗi.
A karshe ya yaba wa gwamna Malam Umar namadi dangane da kudade masu yawa da ya ware domin ciyar da bayin ALLAH kamar yadda ya saba kowace shekara.
Leave a Reply