KWARTANCI ?: Na taba tafka wa Akpabio mari inji Natasha.

Hassan Turaki.

Na taba yunkurin tsulawa Akpabio Mari saboda yunkurin lalata da ni, inji DANI_Tsohuwar shugaba (NDDC).

Joy Nunieh wacce Itace Tsohuwar Shugaban Hukumar habbaka Yankin Naija Delta (NDDC), ta bayyana ta taba marin Sanata Akpabio a lokacin da yake Ministan NDDC sanadiyar yunkurin yin lalata da ita.

“Me yasa bai fadawa Al’ummar Nageriya ba cewa, Na taba marinsa a gidan shakatawarsa dake Apo? Na mare shi ne Saboda ya dauki niyyar yin lalata Dani da karfe Saboda naki amincewa na karbi kuddinsa muyi lalata”.

Hakazalika Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanata mai Wakiltar Mazabar Kogi Ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.

Ta bayyana cewa ” Ya bukaci muyi kwartanci tun a ranar 8 ga Disamba, 2023, lokacin da ni da mijina muka halarci wata goron gayyatar bikin ranar haihuwar Shugaban Majalisar Dattawa a gidansa da ke Uyo.

Bayan ya nuna min kyawawan kayan cikin gidansa ni da shi, Shugaban Majalisar Dattawa ya fada min cewa, tun da yanzu ni ma sanata ce, zai ware lokaci domin mu ji daɗi tare a Uyo.

Inji Natasha Akpoti-Uduaghan
Sanata mai Wakiltar Mazabar Kogi Ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *