Ibrahim A. Makama
Gidauniyar Raudatussahaba Charity Foundation dake unguwar Rimin Kebe, Jihar Kano, ta raba tallafin tufafi ga marayu 148 a karo na goma, domin rage musu radadin rayuwa da kuma sanya farin ciki a zukatan su.
Shugaban gidauniyar, Malam Muslim, ne ya jagoranci rabon tufafin, inda ya bayyana cewa wannan shiri na taimakon marayu yana gudana duk shekara, da nufin tallafa musu.
Shi ma Malam Yakubu Sautussunnah, yayin da yake tsokaci, ya jaddada muhimmancin kulawa da marayu, yana mai cewa al’uma na da hakkin taimaka musu domin kyautata rayuwar su.
A karshe, marayun da suka amfana daga tallafin, sun nuna matuƙar farin cikinsu, tare da yin addu’a ga gidauniyar.
Leave a Reply