Hassan Turaki.
Matatar man fetur ta Dangote ta tabbatar da cewa tana da fetur mai yawa a lalitarta da zai ishi buƙatun Najeriya baki ɗaya, kamar yadda shugaban kamfanin Aliko Dangote ya bayyana.
Da yake magana a ƙarshen mako, Dangote yace matatar na da mai sama da lita miliyan 500.
Kalaman nasa na zuwa ne daidai lokacin da direbobin manyan motoci masu dakon mai ke yajin aiki a jihar Legas sakamakon abin da suka kira “cin zali” da ‘yan sanda ke yi musu a titunan birnin.
Dangote ya kada baki yace “Yanzu da muke magana, muna da lita sama da rabin biliyan. Matatar na samar da albarkatu isassu kamar fetur, da dizel, da kalanzir domin amfanin ‘yan Najeriya dari bisa dari,” in ji Dangote.
Ya faɗa wa tawagar wakilai daga ƙasar Zambia cewa “da ma matatar an yi ta ne ba don Najeriya kawai ba, an yi ta ne domin amfanin Afirka baki ɗaya”.
Leave a Reply