Hassan Turaki.
Yan sanda sun kama wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan.
’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu, lamarin da ya faru a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo.
Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta.
Ya ce, al’umar yankin sun nemi su halaka shi saboda saran matar tasa da ya yi da makami, amma ya sha da kyar.
Leave a Reply