Hassan Turaki.
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta amince da N284,122,002.61 don gina Cibiyar Lafiya matakin Farko a Rimin Zakara, karamar hukumar Ungoggo a jihar.
GuaranteeNews ta ruwaito cewa, a kwanakin baya akalla mutane uku ne suka rasa rayukan su bayan da jami’an tsaro suka bude wuta yayin da mazauna Rimin Zakara suka yi kokarin hana rusau da ake zargin Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta gudanar.
Lamarin yayi matikar hankali da kawo firgici a jihar, wanda hakan ya sa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga tsakani, inda ya yi alkawarin samar da asibiti da masallaci a yankin.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron majalisar a ranar Juma’a, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa kudaden na daga cikin N33,455,431,626.56 da aka ware don aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a fadin jihar.
Ya ce aikin cibiyar lafiyar za a gudanar da shi ne ta karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar.
Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar ta amince da N434,339,301.25 don gyare-gyare da sabunta gine-gine a Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati (GGSS) da ke Shekara, da kuma N893,109,270.55 don gyaran Kwalejin First Lady dake Magwan.
Leave a Reply