NEJA: An rasa rayukan mutane 12 a wani hatsarin mota …

The Editor.

Akalla mutane 12 ne suka rasu a wani Mummunan hatsarin mota a jihar Neja. Hatsarin wanda ya yi sanadiyyar rasuwar wasu mata hudu da maza takwas a hanyar Lapai zuwa Agaie a jihar Neja.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana wa GuaranteeNews cewa, daga cikin mata hudu da suka rasu, uku duka ‘yan gida daya ne.


An kuma rawaito rasuwar wasu mutane uku da suka hada da mata biyu da direban motar da wasu da suka samu raunuka a wurare daban-daban, wanda a yanzu haka suna samun kulawa a babban asibitin Lapai.

Hatsarin ya auku ne a sakamakon wani karo da wata motar fasinja mai dauke da mutane 15 ta yi, da wata tirela a kauyen Nami da safiyar Asabar.

Da yake zantawa da wakilin guaranteeNews daga gadon asibiti ta wayar tarho, direban mai suna, Mohammed Baba, yace ya taso ne daga dajin Kasuwar Gwari dake Minna, babban birnin Jihar Neja, kan hanyar sa ta zuwa Katcha, karamar Hukumar Katcha. Yace direban tirelar yayi yunkurin wuce wata mota, inda ya kara da cewa kokarin da ya yi na kula da motar bus din ya ci tura, wanda hakan ya haifar da hatsarin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *