RASUWA: Sanata lawal yahaya gumau ya kwanta dama …

Hassan Turaki.

Mun Samu tabbacin labarin rasuwar
Tsohon Sanatan da ya wakilci yankin Bauchi ta kudu a majalissar dattawan Nigeria Sanata Lawal Yahaya Gumau, a cikin daren da ya gabata da ƙarfe 3 :45 a birnin tarayya Abuja.

Bayan fama da rashin lafiya kamar yadda maku sancin sa ya sheda wa gidan jaridar guaranteeNews.

lawal ya rasu yana da shekaru 57 a duniya. ya bar mata biyu da yara 8.

Kafin ya zama Sanata, ya zama dan majalisar dokokin tarayya da ya wakilci karamar hukumar Toro a zauren majalissar tarayya daga 2011 zuwa 2018.

Sanata Lawal Gumau ya fara zama a kwaryar majalisar dattawa ne a 2018 bayan da ya samu nasara a zaɓen cike gurbin kujerar sanatan biyo bayan rasuwar Sanata Ali Wakili dake kan kujerar a wancan lokaci. Ya sake samun nasara aka zaɓe shi a babban zaben 2019 har zuwa 2023.

Sai dai duk ƙoƙarin da Lawal Yahaya Gumau ya yi na zarcewa a matsayin sanata a 2023 lamarin ya gagara har ta kai ya fice daga jamiyyar APC ya koma jam’iyyar NNPP domin yin takara amma bai samu nasara ba. Daga baya ya koma jam’iyyar PDP bayan kammala zaɓen 2023.

Tuni dai anyi masa sallah a yau Asabar a birnin tarayya Abuja Masallacin kofar Gidan sa dake Gwarimpa da karfe 1:00pm.

Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa ya sa aljanna firdausi ce makomar sa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *