Hassan Turaki.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bada umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar daga ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025.
Caleb ya yanke wannan shawarar ne saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba wanda ke da alaƙa da laifuka da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Gwamnan, ya kara da cewa yawan baƙi da ke shiga yankunan da ake haƙar ma’adanai na ƙara haddasa matsalar tsaro, domin shawo kan wannan matsala, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciki waɗanda ke da izinin haƙar ma’adanai da kuma ƙirƙirar tsarin kula da ayyukan haƙar.
Gwamnan ya ƙara da cewa za su yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da tsare-tsaren doka da kuma inganta matakan tsaro.
Leave a Reply