Hassan Turaki
Ɗan majalisar wakilai ya fice daga NNPP zuwa APC ‘bisa umarnin al’ummar mazaɓar sa’
Yusuf shitu Galambi dan majalisar wakilai ya sauya sheka daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Tajudeen Abbas, shugaban majalisar ne ya sanar da sauya shekar Shitu Galambi a wata wasika da aka karanta a zauren majalissar yayin zaman ta na ranar alhamis.
Dan majalisar shi ne ke wakiltar mazabar tarayya ta Gwaram a jihar Jigawa.
Galambi yace dole ne ya sauya sheka domin biyayya “umarni” daga mazabar sa.
Ya kuma danganta kudurinsa na barin jam’iyyar NNPP da rikicin shugabancin jam’iyyar da yace yaki ci yaƙi cinyarsa.
Leave a Reply