Ashiru Gambo.
Kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44 (ALGON) ta zabi Shugabar karamar hukumar Tudun Wada Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u a matsayin shugaba.
Kazalika shugabannin kananan hukumomin sun zabi Shugaban karamar hukumar Danbatta Jamilu Abubakar Danbatta a matsayin mataimakin shugaba daga yankin Kano ta arewa sai Alhaji Yusuf Imam Ogan Boye a matsayin mataimakin shugaba daga Kano ta tsakiya, da kuma shugaban karamar hukumar Ajingi Abdullahi Zubair Chula a matsayin mataimakin shugaba daga yankin Kano ta Kudu.
Kungiyar ta kuma zabi Shugaban karamar hukumar Bichi Alhaji Hamza Sule Maifata a matsayin Sakataren kungiya.
A nasa bangaren, gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya shugabannin da aka zaba murna tare da fatan zasu rubanya kokari wajen aiwatar da ayyukan cigaba a yankunan su da kuma hada Kan yan Jam’iyya baki daya.
Leave a Reply