KANO: Mutane 2,369 zasu samu kudaden su …

Hassan Turaki.

Gwamnan Kano ya amince da biyan ƴan shara mutum dubu biyu da dari uku da sittin da tara (2,369) albashin da su ke bi na watanni tara (9).

Majalissar zartaswar jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba kabir, ta amince da biyan bashin albashin watanni tara ga ma’aikatan shara guda 2,369 a fadin jihar.

Biyan ya ƙunshi haƙƙunan su daga Yuni, 2024 zuwa Fabrairu, 2025.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Dahir M. Hashim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

A cewar sa, amincewar wani gagarumin yunkuri ne na taimaka wa wajen dorewar lafiyar muhalli a jihar.

Ya yaba da yadda jihar ke ci gaba da kokarin inganta rayuwar al’ummar ta da kuma tsaftar muhalli.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *