NMDPRA: An dauki matakin dakile gobarar tankokon man fetur …

Hassan Turaki.

Hukumar kula da dakon man Fetur (NMDPRA) ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan uku na shekarar 2025, za’a hana manyan motocin tankokin mai masu daukan lita 60,000 zirga-zirga a kan titunan Najeriya. Wannan mataki yana da nufin rage yawaitar hadurran manyan motocin mai, waɗanda ke haddasa gobara da asarar rayuka, kana daga karshen shekarar 2025, an haramta lodin fiye da lita 45,000 na mai a kowaccee matatar lodin kayayyaki.

Shugaban rarraba kayayyakin man fetur a NMDPRA, Ogbugo Ukoha, ya bayyana cewa matakin ya zama dole sakamakon yawaitar haɗurran manyan motocin dakon mai a ƙasar, ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro, hukumar FRSC, da ƙungiyoyin NARTO da sauran masu ruwa da tsaki a harkar safarar mai.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *