Hassan Turaki.
A yau ne Maimartaba Sarkin Dutse Alhaji Muhammad Hamim Nuhu Sunusi ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano bayan da ya taso daga filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja.
Maimartaba sarki ya samu tarba daga yan majalissar sarki da sauran manya daga masarautar dutse.
Sannan yayi godiya ga ALLAH da ya bashi damar habbaka zumuncin dake tsakanin masarautar dutse da masarautun arewacin Nigeria musamman sarakan da ya gana dasu.
Muna addu’ar ALLAH ya kara wa sarki lafiya da nisan kwana me amfani.
Leave a Reply