By Hassan Turaki.
Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48.
Haɗarin wanda ya faru ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, a Hotoro.
A cewar Hukumar FRSC, haɗarin ya rutsa da wata motar tirela ƙirar DAF ɗauke da kayayyaki da fasinjoji, inda bincike na farko ya nuna cewa direban ya yi tuƙin ganganci saboda gudu wanda hakan ya sa motar ta kauce hanya ta afka ƙarƙashin gadar.
Rahotanni sun nuna cewa, adadin waɗanda haɗarin ya rutsa da su ya kai 71, mutum 48 ne suka jikkata, yayin da 23 suka mutu.
Leave a Reply