AN KUMA: Ku wakilan mu ne kar ku zubar mana da mutunci, Lamido ya jan kunnen Ribadu …

Hassan Turaki.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Kuma tsohon Ministan Harkokin wajen Nageriya Sule Lamido A lokacin da yake mayarda martani ga dambarwa Tsakanin Mai bawa Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro Nuhu Ribadu da Kuma kasar Kanada Yana Mai cewa NSA da Shugabansa dole ne su fahimci cewa suna wakilta Ayyukanmu ne darajar kasarmu ne a matsayin al’ummar kasa mai wayo!

Shekaru biyu da suka gabata sun tsumduma rikici da kungiyarmu ta dangantakarmu ta duniya da kuma ECOWAS kuma yanzu da Kanada Yakamata duk wata Hauragiya ta tsaya tunda An bayar da izinin zama a duk lokacin da aka yarda ga ma’aikatar harkokin kasashen waje don basu damar taka rawar su a matsayin masu bibiyar kare mu a matakin duniya.

Tsoma bakin me baiwa shugaban kasa shawara dangane da tsaro kan rikicin Hana Visa ga Sojoji abu ne da yakamata Ma’aikatar Harkokin Waje ta magance ta Hanyar kwamishinan Harkokin waje tare da tunkarar sa da magana Mai kyau domin cimma matsaya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *