HARAJI: Kudirin harajin tinubu ya tsallake karatu na biyu a majalissar wakilai …

Hassan Turaki.

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da ƙudirin haraji a karatu na biyu, bayan zazzafar muhawara kan ƙudirin tsakanin ‘yan majalisar.

Tun da farko majalisar ta haɗe duka ƙudurorin harajin huɗu da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya aike mata a shekarar da ta gabata zuwa ƙuduri guda kafin fara muhawara a kansa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne ya jagoranci muhawarar, wanda ya ce kuɗurin zai taimaka wajen farfaɗo da fannin karɓar haraji na ƙasar.

Farfesa Ihonvbere ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin bisa kwaskwarimar da suka yi wa ƙudurin, da nufin ,magance matsalolin da aka yi fargabarsu tun da farko.

Ƙudirin harajin ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin ‘yan ƙasar, musamman waɗanda suka fito daga yankin arewacin ƙasar, inda suka riƙa zargin cewa sabon ƙudirin zai cutar da yankin.

A farkon wannan shekarar ne ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka amince da kuɗurin bayan sun yi masa kwaskwarima dangane da yadda za a raba harajin VAT.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *