Hassan Turaki.
Gwamnatin jihar Neja ta kammala shirinta na zabge farashin kayan masarufi saboda zuwan watan azumin ramadan.
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ne ya sanar da hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar gidauniyar ‘Gates’ a fadar gidan gwamnati dake Minna.
Gwamna Bago yace ya ɗauki matakin ne domin sauƙaƙa wa al’umma a lokacin azumin watan Ramadan.
Leave a Reply