Hasaan Turaki.
‘Yan bindiga sun sace Dr. Adekunle Raif Adeniji, babban darakta a hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja, na tsawon makonni biyu, suna bukatar kuɗin fansa har Naira miliyan dari uku da hamsin (350).
Wannan sace-sacen na ƙara jaddada yawaitar garkuwa da manyan mutane a ƙasar nan. Kwanan nan, an sace tsohon Birgediya-Janar Maharazu Tsiga, tsohon Darakta Janar na Hukumar NYSC, a gidan sa dake Katsina. Masu garkuwar sun bukaci Naira miliyan dari biyu da hamsin (250) domin sakin sa.
Leave a Reply