KANO: Anyi kira ga matsakaita da kananan yan kasuwar kurmi da …

Hamza Musa Garba.

Karamar hukumar birnin jihar Kano ta yabawa matsakaita da kuma manyan ‘yan kasuwar Dubai da na ‘yan kasuwar Kurmi bisa goyon baya da hadin kan da suke bayar wa ga karamar hukumar birnin jihar Kano wajen bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga domin cigaban yankin.

Mai ba da shawara ta musamman ga karamar hukumar birnin jihar Kano a kan harkokin kasuwannin yankin, Hajiya Mariya Ali Zage ce, ta bayyana hakan a lokacin da ta ke ganawa da shuwagabannin kungiyoyin kaauwannin biyu

Hajiya Mariya Ali Zage ta jaddada cewa karamar hukumar ta himmatu wajen yin amfani da kudaden shiga da aka kirkiro domin gudanar da ayyukan cigaba masu ma’ana wadanda za su amfanar da al’ummar yankin.

Ta kuma bukaci mazauna yankin karamar hukumar birni da su ci gaba da tallafawa tare da bada hadin kai ga gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf domin cimma manufofin da ta sa a gaba . Ta mai kuma karfafawa ‘yan kasuwannin da su marawa tsare tsaren gwamnati baya domin kawo cigaba da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Da suke jawabi, shugaban Kasuwar Dubai Alhaji Ibrahim Usman Shaishai da mataimakin shugaban kasuwar Kurmi Alhaji Munzali Babba, sun jaddada kudurinsu don tallafawa ayyukan gwamnati na cigaba tare da yin kira ga mutane su ci gaba da tallafawa manufofin gwamnatin jihar kano don samun ci gaban a yankin karamar hukumar birnin jihar Kano.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *