Editor.
Fitaccen mai bincike kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama ɗan asalin Najeriya, mazaunin kasar Ingila, Dr. Idris Ahmed ya bayyana wasu muhimman zarge-zarge da ya sani akan Malam Nuhu Ribadu mai taimakawa Shugaban kasa kan sha’anin tsaron Najeriya.
Dr. Idris ya bayyana cewa, “A lokacin da yake shugaban hukumar EFCC, ya karbi makudan kudaden cin hanci. Musamman dalar Amurka, akwai wani wanda Shi ne me yiwa Nuhu Ribadu canjin dalar Amurka, tsohon dan sanda ne ACP mai ritaya ne ana kiransa da suna (retired) Rabiu Abubakar Shariff.
Dr. Idris Ahmad ya kara da cewa; Rabiu Abubakar Shariff shi clasmate dina ne lokacin muna karatun sakandare. Shine wadda Lieutenant General Tukur Buratai ya turo shi zuwa kasar Burtaniya, domin ya saci salulata. Wanda Bai yi nasaran yin hakan ba Har Allah ya tona masa asiri. amma sunyi nasaran hacking salulan daga bisani.
A lokacin da Rabiu yake canjawa Ribadu kudi a kasuwan canjin dollar dake Obalande Lagos, yana zaune ne a boys quarter na gidan babban yayanmu, marigayi injiniya, Ahmed, a Victoria Island, dake Legas,
Wannan shi yasa nake da cikakken bayani game da jagwal da Malam Nuhu Ribadu yayi da Rabiu Abubakar Shariff mai canjin dala.
Yanzu haka da muke magana, Rabiu Abubakar Shariff shine mai baiwa Nuhu Ribadu shawara akan tsaro!
Jama’a, da irin wannan shugaban kasan, da NSO nashi, da mai baiwa NSO shawara akan tsaro, ta ina ne Najeriya zata ci gaba? Dukkansu ukun azzalumai ne, maciya amanan Najeriya da al’ummanta. Inji Dr. Idris Ahmad.
Leave a Reply