Politics
Kwankwaso ya gana da Aregbesola a Lagos …


Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida na ƙasar, Rauf Aregbesola a birnin Legos da ke kudancin ƙasar.
Cikin wani saƙo da Kwankwason ya wallafa shafinsa na X, ya ce sun yi ganawar ne domin tattauna batutuwan da suka sfahi siyasa da makomar dimokraɗiyyar ƙasar.
Ganawar ‘yan siyasar biyu na zuwa a daidai lokacin da jam’iyyun hamayya ke ta kiraye-kiyare ga jam’iyyun hamayya su haɗa kai don tunkarar zaɓen 2027.
A watan da ya gabatane ne jam’iyyar APC resehn jihar Osun ta sanar da korar Aregbesola – wanda tsohon gwamnan jihar ne – bisa zarginsa da laifin cin amanar jam’iyyar.