Naziru Hamisu.
Ministan tsaron Nigeria Alh. Muhammad Badaru Abubakar (Mon, mni) ya ziyarci tsohon kwamishinan muhalli Hon. Ibrahim Baba Chai-chai a gidansa dake unguwar Hausawa Layout Kano.
Ministan ya ziyarci tsohon kwamishi nan ne domin dubiyar rashin lafiya da yake fama da ita.
Badaru yayi addu’ar neman lafiya da kwarin jiki ga Baba Chai-chai Allah ya bashi3 lafiya yas
Mataimakin gwamnan jihar Jigawa Engr. Aminu Usman Gumel, shugaban jam’iyyar Apc na jihar Jigawa Hon. Aminu Sani Gumel, sakataren kuɗi na jam’iyyar Apc na ƙasa Hon. Bashir Gumel, shugaban rukunin kamfanin Gerawa Alh. Isah Gerawa, Alh. Lawan Ya’u Roni, ƴan majalissun tarayya, ƴan majalissun dokokin jihar Jigawa, tsofin shugabannin ƙananan hukumomi da sauran ƴaƴan jam’iyyar APC ne su raka shi.
A jawabin sa Hon. Ibrahim Baba Chai-chai yayi godiya da karamcin da ya samu ya kara da cewa hakan yana tabbatar da zumunci da rikon amana.
Leave a Reply