Politics

TATTAKI: Ina cikin koshin lafiya kuma na shiga yankin Kano – inji Lawan

Matashi lawan Habibu yace soyayyar da yake yiwa Abba tafi ƙarfin ya fasa tattakin sa saboda matsalar tsaro.
Lawan ya kara da cewa na amsa kiraye-kirayen waya da dama na karfafa gwiwa da akasin haka kuma ina godiya duk mun hadu ne a fagen soyayyar gwamna dan baiwa me dumbin masoya gida da waje.

Habibu yace tuni dai tafiyar sa tafi rabi domin kuwa ko yanzu haka yana cikin jihar Kano kasancewar ya shiga karamar hukumar gaya ta jihar Kano kuma duk kalaman da akayi a dandalin sada zumunta sun kara masa karfin gwiwa.

Matashin yana kara sanar da al’uma cewa yana cikin koshin lafiya gami da nishadin kasancewar sa a hanyar zuwa karrama Gwamna dan baiwa me tarbiyyar siyasa irin ta darikar kwankwasiyya wacce take dauke da amana.

Zamu ci gaba …

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button