Business
DANGOTE: motocin dakon mai masu amfani da CNG …

Hassan Turaki.
Motocin dakon Man Fetur masu amfani da iskar gas ɗin CNG na kamfanin Dangote sun iso Nijeriya
Rahotanni sun nuna cewa motocin da zasu rika dakon Man Fetur kyauta a faɗin Nijeriya, na Kamfanin shahararren ɗan kasuwan nan Alh. Aliko Dangote sun iso birnin Ekko dake jihar Legas.
Motocin da yawan su yakai guda 4,000 zasu riƙa dakon Man Fetur kyauta suna kaiwa sassan Nijeriya. Wanda hakan zai samar da gagarumin sauki na farashin man fetur a Nigeria.