Security

Kotu ta tura matashi gidan yari bayan zargin yaɗa mutuwar Tinubu a TikTok

Hassan Turaki.

Wata Babbar Kotun Majistare da ke Abuja ta bayar da umarnin a tsare wani mashahurin mai amfani da kafafen sada zumunta, Ghali Isma’il, a Gidan Gyaran Hali na Keffi saboda yada karya cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mutu bayan fama da wata mummunar rashin lafiya.

Jami’an ƴan sandan farin-kaya (DSS) ne su ka kama Ghali Isma’il, wanda ya wallafa wannan ikirari a TikTok mai suna @bola_asiwaju, bayan bazuwar faifen bidiyon.

Daga bisani sai SSS ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi yada ƙarya da kuma tunzura jama’a da ƙiyayya ga gwamnati.

Tuhuma ta Ɗaya – Yada Labarin Ƙarya da Nufi Tayar da Hankalin Jama’a:

Bayan sauraron hujjoji daga bangaren masu kara da lauyoyin kare wanda ake tuhuma, alkalin da ke jagorantar shari’ar, Ekpeyong Inyang, ya ƙi bayar da beli, ya kuma bayar da umarnin a cigaba da tsare Ghali Isma’il.

An dage shari’ar zuwa 19 ga Agusta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button