Health
TSAFTAR MUHALLI: An tura manajan kamfani da ma’aikatan sa gidan yari …

Hassan Turaki.
Manajan wani kamfanin sarrafa sinadarin Monoxide da sauran ma’aikatansa zasu shafe watanni uku a gidan gyaran hali da tarbiyya bayan samunsu da laifin karya dokokin tsaftar muhalli na wata wata a Bauchi.
Kotun tafi da gidan ka na hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Bauchi ce ta samu matasan da aikata laifin da suka amsa ba tare da wahalar da kotu ba, inda kuma suka nemi sassauci a hukuncin da za a yanke musu.
Hakan ne yasa kotun ta yanke musu hukuncin shafe watanni uku a gidan gyaran hali da tarbiyya ko zabin biyan tara na Naira Dubu Dari biyu.