News

AMBALIYA: An rasa rayuka da duniyoyi a jihar Neja …

HASSAN TURAKI.

Wasu mutum 12 ’yan gida daya da almajirai sama da 50 na cikin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwan da ya afka wa yankin Tiffin Maza da unguwan Hausawa na karamar hukumar Mokwa a jihar Neja ranar Larabar da ta gabata.

Ambaliyar, wacce ta biyo bayan wani mamakon ruwan sama da aka tafka a daren na Laraba, ta kuma lalata dukiyoyi da dama, yayin da har yanzu ake ci gaba da neman wasu mutanen da suka bace.

Jaridar GuaranteeNews ta gano cewa akasarin wadanda iftila’in ya fi shafa mata ne da kananan yara.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da mutuwar mutum 21, amma mutanen yankin sun ce wadanda suka mutu za su iya haura 60.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button