News

HAJJ 2025: Anyi kira ga Alhazan jihar Jigawa …

Alh. LUKMAN MALAM HASSAN.

An bukaci maniyyatan Jihar Jigawa dasu ci gaba da kasancewa masu juriya da hakuri a yayin gudanar da aikin Hajji.

Amirul-Hajji na Jihar Jigawa kuma Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussain Adamu yayi wannan bukata lokacin da ya ziyarci Maniyyatan a Masaukin su dake Birnin Madina.

Ya kara da cewa aikin Hajji yana bukatar juriya da hakuri da bin doka da oda domin yin aikin Hajji karbabbiya.

Mai Martaba Sarki ya yabawa maniyyatan bisa yadda suke nuna ladabi da biyayya da sanin yakata da bin dokakin kasar Saudiyya, inda yayi fatan hakan zai dore a zaman da za suyi na birnin Makkah domin cigaba da gudanar da aikin Hajjin wannan shekara.

A jawabin Darakta Janar na Hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya godewa Amirul-Hajji na Jiha bisa yadda yake kula da Maniyayatan tun daga daga Najeriya har Zuwa Kasar Saudiyya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button