BINCIKE: An samu cushe cikin kasafin kudi …

HASSAN TURAKI.
Rahoton wata ƙungiya mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka (BudgIT) ya gano cewa wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya na cusa kwangiloli marasa amfani, waɗanda ba su da alfanu ga ƙasa a cikin kasafin kuɗin Najeriya.
BudgIT ta ce ta gano kwagiloli har 11,122 wadanbda zasu lashe kuɗin da ya haura naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kuɗin 2025 da Majalisar ƙasa ta cusa ba tare da la’akari da cancanta ba.
Haka nan rahoton ya bayyana cewa an cusa irin wadannan ayyuka a kasafin hukumomi da ma’aikatun gwamnati waɗanda ba su da wata alaƙa da ayyukan.
Majiyar mu ta rawaito cewa, wasu daga cikin kwangilolin da aka lissafa sun haɗa da kwangilar bayar da tallafin karatu da rabon takin zamani da gina cibiyar koyar da kwamfuta ICT/CBT, da kuma samar da motoci don tsaro da sauransu duk da cewa babu alaƙar waɗannan kwangiloli kai tsaye da ayyukan ma’aikatun.
BudgIT ta bayyana cewa waɗannan ƙwangiloli da aka saka cikin kasafin kuɗi sun kai kashi 12.5 cikin 100 na jimillar naira tiriliyan 54.99 da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa irin waɗannan kwangiloli na rage tasirin amfani da kuɗin gwamnati yadda ya kamata, kuma suna rushe amana tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.
Irin waɗannan kwangiloli da ake cusawa cikin kasafin kuɗin Najeriya sun daɗe suna faruwa tun bayan dawowar demokraɗiyya a Najeriya a 1999.
BudgIT ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ba da muhimmanci ga gaskiya da gaskiyar lissafi a tsarin kasafin kuɗi, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen gwamnati na tafiya ne wajen ayyuka da ke amfanar da al’umma kai tsaye.