BORNO: Zulum ya kara mika roko ga gwamnatin Tinubu …

HASSAN TURAKI.
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya roƙi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya daina Siyasantar da matsalar tsaro a arewacin Najeriya Musamman a jihar Borno.
Wannan yazo ne yayin wani hira da ya gudanar bayan dawowarsa daga inda Boko Haram suke neman mamayewa a jihar, Gwamnan ya tona asiri tare da ya bayyana gaskiyar abinda yake faruwa
Zulum ya shaida wa duniya ba tare da tsoro ba cewa akwai manyan ‘yan siyasa da manyan jami’an sojojin Nigeria wanda suke da hannu da taimakawa kungiyar Boko Haram da kudi da makamai da bayanan sirri.
Gwamna Zulum ya bayyana takaicin sa akan yadda Shugaban Kasa Tinubu yake tafiyar hawainiya game da yaki da Boko Haram, ya roki Tinubu akan ya dinga sauraran wadan da zasu fada masa gaskiya akan wannan matsala.
Gwamnan ya roki Shugaban Kasa Tinubu akan ya dena siyasantar da matsalar tsaron Arewa, ya roki a bawa Sojoji manyan makamai na yaki, domin makaman da suke hannun Boko Haram yafi na Sojojin da suke fagen daga karfi.
Zulum yace ina mai tabbatar muku Sojoji basu da kayan fada na zamani irin wanda ‘yan ta’adda suke da shi, domin yanzu ‘yan ta’adda na amfani har da fasahar zamani wajen yakar Sojoji da kaddamar da hare-hare
Gwamna Zulum yace ya kamata Shugaban Kasa ya saurari bukatun Sojoji, domin Sojoji sun fi kowa sanin yadda za’ayi maganin ta’addancin nan, za’ayi nasara akan Boko Haram domin kwangila ce, da zaran an cire kwangilar da almundahana a cikin ta’addancin za’a kawo karshensa, inji Gwamna Zulum