Security

Za’a sanya gidaje 753 na Emefiele a kasuwa …

HASSAN TURAKI.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta sayar da gidaje 753 da aka ƙwato daga tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Wannan sanarwar ta fito ne daga Ministan Gidaje, Ahmed Dangiwa, a ranar Talata yayin da yake karɓar takardun mallakar gidajen daga hannun Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati wato (EFCC).

Ministan, ya gode wa EFCC saboda yadda take aiki tuƙuru wajen yaƙar cin hanci da rashawa.

A cewar sanarwar da kakakin ma’aikatar, Salisu Haiba, ya fitar yace an tabbatar cewa waɗannan kadarori na daga cikin dukiyoyin da aka ƙwato daga hannun masu almundahana da kuɗaɗen kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button