Ibrahim Adamu Dutse.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da kashe Naira biliyan 80 don sake gina madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev ne ya bayyana haka a ranar Talata bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya karo na biyu wanda shugaba Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Utsev ya ce, gwamnatin jihar Borno na hada kai da gwamnatin tarayya domin fara aikin da aka shirya gudanarwa cikin watanni 24 masu zuwa.
Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025.
Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Leave a Reply