NWDC: Walin Kazaure ya hau sabuwar kujera a majalissa …

Ibrahim A. Makama

Majalisar Dattijai ta naɗa Sanata Babangida Hussaini (Walin Kazaure) da ke wakiltar Jigawa North West a matsayin Ciyaman na Kwamitun Majalisar Dattawa na Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma wato North West Development Commission (NWDC).

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Obot Akpabio ne ya bayyana hakan a yayin zaman Majalisar a safiyar Talata.

Sanata Babangida kafin wannan sabon muƙamin shine Ciyaman na Kwamitin Majalisar Dattawa na Hukumar kula da titunan Tarayya (FERMA). Ya kuma riƙe Babban Sakataren Ma’aikatar tsaro da kuma Ma’aikatar Ayyuka ta ƙasa.

Hukumar ta NWDC wacca Shugaban Ƙasa ya tabbatar da ita a doka bayan da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya gabatar da ƙudurin kafa ta a gaban Majalisar, zata yi aiki ne a dukkan jihohi 7 dake Arewa Maso Yamma da Hedikwatar ta a Jihar Kano.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *