Ibrahim Adamu Dutse.
Jami’an Rundunar ‘Yansandan Jihar Adamawa, sun harbe wani da ake zargi da garkuwa da mutane tare da cafke wani, sannan sun ƙwato makamai.
Rundunar ta ce jami’anta na sashen yaƙi da garkuwa da mutane, tare da haɗin gwuiwar ‘yan sa kai, sun kai sumame a mafakar masu garkuwa da mutanen da ke tsaunin Holma a ƙaramar hukumar Song.
A cewar jami’in, yayin da ‘yan bindigar suka hango su, sai suka buɗe wuta don kaucewa kamun su, wanda a yayin musayar wutar, suka kashe ɗaya daga cikinsu masu garkuwa da mutanen, sauran kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga, kana suka kama daya daga cikinsu mai suna Mohammed Sale.
Jami’an tsaron sun yi nasarar ƙwato makamai daga da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda daya, bindigogi biyu da aka kera a gida, da tarin alburusai.
Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar, CP Dan kombo Morris, ya jinjina wa jami’an kan nasarar da suka samu kana ya buƙaci su ci gaba da haɗin gwiwar don kawar da ‘yan ta’adda da tabbatar da tsaron al’umma, wanda ya ce ana ci gaba da bincike, tare da kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani mutum da ke da raunukan harbin bindiga ko wani abu da ake zargi.
Leave a Reply