Hassan Turaki.
Kungiyar habbaka dimokradiyya a arewacin najeriya tayi ALLLAH wadai da kama Farfesa Usman Yusuf daya daga cikin masu fashin baki kan al’amuran siyasa a Najeriya.
Kakakin kungiyar ta LND Dr. Ladan Salihu ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a wata kafar talabijin inda yace doka ba tace aje har gida a dauki mutum a cikin iyalansa ba tare da takardar shaidar gayyatar sa zuwa amsa tambaya ba.
Ladan ya kara da cewa wannan ba abune da zai hana yan gwagwarmaya fada wa gwamnati gaskiya ba.
Dr. Ladan Salihu wanda yayi magana da yawun kungiyar ta (LND) yayi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bada umarnin gaggawa domin a hanzarta sakin Farfesa Usman Yusuf, haka kuma yayi kira ga shugabannin tsaro a Najeriya da suji tsoron ALLAH suyi aikin su bisa gaskiya da adalci.
A karshe Ladan Salihu yace kama daya daga cikin su tamkar buɗe kafar adawa ce babu gudu babu ja da baya.
Leave a Reply