Hassan Turaki.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cika hannu da wasu matasa biyu mace da namiji bisa zargin yin aure a asirce ba tare da sani ko amincewar iyayensu ba.
Mataimakin babban kwamandan hukumar Hisbah, Sheikh Mujahidden Aminudeen ne ya tabbatar da kamen matasan da bayyana auren a matsayin wanda ya sabawa addinin musulunci kuma ba za a yarda da shi ba.
A cewar Aminuddeen, ma’auratan da aka sakaya sunansu, rahotanni sun bayyana cewa an daura aurensu ne a wani wurin shakatawa bayan wanda ya jagoranci daurin auren ya biya sadakin amaryar a daren Laraba.
Aminuddeen ya nanata cewa aure abu ne mai tsarki a addinin musulunci, don haka, hukumar ba za ta lamunci duk wani wulakanci ga addinin ba.
Leave a Reply