Hassan Turaki.
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana bisa zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi.
Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa.
Leave a Reply