Yar shekara 17 daga yobe ta lashe gasar turanci na duniya

Hassan Turaki.
Matashiya ‘Yar Asalin Jihar Yobe, Nafisa Abdullahi Ta Lashe Gasar Turanci Ta Duniya Da Aka Gudanar A Birnin Landan
Nafisa Abdullah Aminu, yarinya ‘yar shekaru 17 daga jihar Yobe, ta samu babban nasara a gasar ƙasa da ƙasa ta harshen Turanci da aka gudanar a London, Birtaniya, ƙarƙashin TeenEagle Global Finals 2025.
Nafisa, wadda ke karatu a Nigerian Tulip International College (NTIC), Yobe, ta fice daga cikin fiye da ɗalibai 20,000 daga ƙasashe 69 – ciki har da waɗanda harshen Turanci ke matsayin na uwa-uba a wurinsu.
Wannan gagarumar nasara da ta samu ana kallonta a matsayin abin alfahari ga Najeriya da nahiyar Afrika gaba ɗaya, duba da asalin jihar da ta fito wadda ke fama da ƙalubale a harkar ilimi da tsaro.
A sakamakon haka, hukumomi da malamai a jihar Yobe sun nuna farin ciki da wannan nasara, suna fatan za ta zama abin ƙarfafa guiwa ga sauran matasa domin yin fice ta hanyar ilimi da ƙoƙari.