TATTAKI: Na shigo birnin dabo, Inji Matashi Lawan

EDITA.
Matashin da ya taso daga jihar Jigawa zuwa Kano ya isa birnin ta Kano kamar yadda yadda ya kudiri aniyar sa ta shiga Kano ta hanyar tattaki.
Lawan yace “ina shaida wa al’umar Kano musamman masoyan gwamna abba Kabir Yusuf da sukayi ta karfafawa mun gwiwa cewa na isa Kano lafiya kuma kowani lokaci daga yanzu zan je kofar gidan gwamnatin jihar Kano domin shiga na aiwatar da abinda ya kawo ni”
Matashin ya bayyana haka ne yayin ganawar sa da gidan jaridar GuaranteeNews ta wayar salula.
Ya kara da cewa yaga sakonni da dama a shafukan sada zumunta dangane da tafiyar sa ta tattaki kuma duk kalaman sun kara masa kwarin gwiwa ne kamar yadda yace.
Haka zalika ya jinjina wa manema labarai da suka bashi cikakkiyar kulawa ta hanyar bibiya da kuma yada labaran tafiyar sa.
Zamu ci gaba …